October 18, 2025

Sojojin Isra’ila Sun Ƙara Luguden Wuta A Gaza Yayin Da Adadin Mutanen Da Suka Mutu Ya Ƙaru

AP25231275851186-1755605233

Jiragen yaƙi da tankokin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a Birnin Gaza domin ƙwace iko da yankin.

Mazauna yankin sun ce kusan Falasɗinawa miliyan ɗaya da ke zaune a wurin suna jin rugugi ba dare ba rana a arewaci da gabashin birnin.

Dakarun Isra’ila sun kuma sake komawa sansanin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza a yayin farmakin.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, a cikin awanni 24 da suka gabata kaɗai, an kashe Falasɗinawa 64 tare da jikkata kusan 300.

Haka kuma ta ce tun daga watan Oktoban 2023 zuwa yanzu, adadin mutanen da Isra’ila ta kashe ya kai 62,686, yayin da 157,951 suka jikkata sakamakon hare-haren.