October 18, 2025

Shin kun san ministocin da Tinubu ya sallama da waɗanda ya naɗa?

IMG-20241014-WA00031.jpg

Daga Sabiu Abdullahi


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministocinsa biyar tare da naɗa sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma’aikatu.

Fadar gwamnatin Najeriya ce ta fitar da sanarwar a shafinta na X (tsohon Twitter).

Ministocin da aka sallama:

1. Barr. Uju-Ken Ohanenye – Ma’aikatar Harkokin Mata


2. Lola Ade-John – Ma’aikatar Yawon Buɗe Idanu


3. Farfesa Tahir Mamman – Ma’aikatar Ilimi


4. Abdullahi Muhammad Gwarzo – Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane


5. Dr. Jamila Bio Ibrahim – Ministar Matasa



Ministocin da aka sauya wa ma’aikatu:

1. Hon. Dr. Yusuf Tanko Sununu – Ƙaramin Ministan Ilimi ya koma Ƙaramin Ministan Jinƙai da Rage Talauci


2. Dr. Morufu Olatunji Alausa – Ƙaramin Ministan Lafiya, ya koma Ministan Ilimi


3. Barr. Bello Muhammad Goronyo – Ƙaramin Ministan Ruwa da Tsafta, ya zama Ƙaramin Ministan Ayyuka


4. Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh – Ministan Raya Naija Delta, ya koma Ministan Raya Yankuna (Sabuwa)


5. Uba Maigari Ahmadu – Ƙaramin Ministan Ƙarafa ya koma Ƙaramin Ministan Raya Yankuna


6. Dr. Doris Uzoka-Anite – Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta koma Ƙaramar Ministar Kuɗi


7. Sen. John Owan Enoh – Ministan Wasanni ya koma Ƙaramin Ministan Kasuwanci da Zuba Jari (Masana’antu)


8. Imaan Sulaiman-Ibrahim – Ƙaramar Ministar Harkokin ‘Yan Sanda ta koma Ministar Harkokin Mata


9. Ayodele Olawande – Ƙaramin Ministan Matasa ya koma Ministan Raya Matasa


10. Dr. Salako Iziaq Adekunle Adeboye – Ƙaramin Ministan Muhalli, ya koma Ƙaramin Ministan Lafiya



Sababbin Ministocin da aka naɗa:

1. Dr. Nentawe Yilwatda – Ministan Jinƙai da Rage Talauci


2. Muhammad Maigari Dingyaɗi – Ministan Ƙwadago


3. Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu – Ƙaramar Ministar Harkokin Waje


4. Dr. Jumoke Oduwale – Ministar Kasuwanci da Zuba Jari


5. Idi Mukhtar Maiha – Ministan Kusa da Dabbobi


6. Hon. Yusuf Abdullahi Ata – Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane


7. Suwaiba Said Ahmad (PhD) – Ministar Ilimi