October 18, 2025

Shettima ya isa ƙasar Sweden domin ziyarar aiki ta yini biyu

IMG-20241017-WA0006.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya isa ƙasar Sweden domin gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki biyu da nufin bunƙasa kasuwanci da hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Mataimakin shugaban ƙasar yana tare da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang;  Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar;  da wasu shuwagabannin hukumomin gwamnati da na ƙananan hukumomi.

Kakakin Shettima, Stanley Nkwocha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka raba ma manema labaru a safiyar yau Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Ziyarar wadda ta biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu, tana da manufar ganin mataimakin shugaban ƙasar ya tattauna da manyan jami’an gwamnati.  Ana sa ran zai gana da Gimbiya Victoria ta Sweden da Firaminista na Sweden.

“Lamuran da ake sa ran samun haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Sweden wanda mataimakin shugaban ƙasa zai gaba da jami’an gwamnatin Sweden a kansu sun haɗa da kimiyyar sadarwa, ilimi, sufuri, noma, da haƙar ma’adanai.”

Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai komo gida ne a ranar Asabar mai zuwa.

1 thought on “Shettima ya isa ƙasar Sweden domin ziyarar aiki ta yini biyu

  1. whoah this weblog is wwonderful i love reading your articles.
    Keep upp thee great work! You recognize, manjy individuals aree seasrching around forr this information,you could aaid
    thhem greatly.

Comments are closed.