January 14, 2025

TikTok ya goge bidiyoyi fiye da miliyan 2.1 a Najeriya saboda take dokokinsa

3
20_42_07_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kamfanin TikTok ya bayyana cewa ya goge bidiyoyi miliyan 2.1 daga shafinsa a Najeriya tsakanin Afrilu zuwa Yuni 2024, saboda take dokokin dandalin.

A cewar rahoton da kamfanin ya fitar a ranar Talata, TikTok ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da ingancin abubuwan da ake wallafawa, da kuma kare masu amfani da shafin.

TikTok ya nuna cewa kashi 99.1 cikin 100 na bidiyoyin an goge su tun kafin a gabatar da ƙorafi, yayin da kashi 90.7 cikin 100 aka goge su cikin awa 24.

Kamfanin ya ce waɗannan matakan suna nuna jajircewarsa wajen hana watsa abubuwan da ke da illa, tare da samar da dandalin da ya dace da masu amfani da shi a Nijeriya.

A duniya kuwa, TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, ciki har da miliyan 144 da na’urorin sa suka gano suna take dokoki.

Har ila yau, kamfanin ya ƙara jaddada kudurinsa na nuna gaskiya da amincin dandalin ga masu amfani daga ko’ina cikin duniya, ciki har da Nijeriya.

3 thoughts on “TikTok ya goge bidiyoyi fiye da miliyan 2.1 a Najeriya saboda take dokokinsa

  1. I’m edtremely impessed with youir writing skills aas well aas
    with tthe layouut on your weblog. Is this a paid theme or did youu customize iit yourself?

    Eitjer waay keep up the excellkent quality writing, itt is raqre
    too seee a nice blig ike thos one today.

  2. Howdy! Thiis blog ppost couldn’t be writteen anyy better!
    Goijg thfough this article reminds me off mmy previous roommate!
    He constanttly keptt peaching aboit this. I mowt certainly
    will forward this posxt to him. Pretty sure he’s goinhg tto have
    a grea read. Many thanks for sharing!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *