October 18, 2025

Shehun Borno yayi kira ga musulmi da su tuba su koma ga Allah

362244646_249142341237142_2723140072414855867_n

Me alfarma Shehun Borno Alhaji (Dr) Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi yayi kira ga al’umar musulmi da su yawaita Istgifari da neman afuwar Allah don samun damina me albarka.

Shehun ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun magatakardar Masarautar Borno Zanna Kazalma ya ƙara da kira ga limaman masallatan Jumu’a da kada su yi ƙasa a guiwa wajen cigaba da jagorantar Sallah da addu’oin roƙon ruwa a daidai wannan lokaci da ake fama da fari a sassan jihar da kewaye.

Ya ƙara da jan hankalin sauran masallatan da ba na Jumu’a ba da su yawaita Zikiri da nafilfili, tare da kiran ɗaukacin al’uma da su kasance masu taimakon marasa galihu tsakanin su, tare da addua’ar ɗorewar zaman lafiya da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

63 thoughts on “Shehun Borno yayi kira ga musulmi da su tuba su koma ga Allah

  1. Great article! I appreciate the clear and insightful perspective you’ve shared. It’s fascinating to see how this topic is developing. For those interested in diving deeper, I found an excellent resource that expands on these ideas: check it out here. Looking forward to hearing others’ thoughts and continuing the discussion!

  2. Great article! I appreciate the clear and insightful perspective you’ve shared. It’s fascinating to see how this topic is developing. For those interested in diving deeper, I found an excellent resource that expands on these ideas: check it out here. Looking forward to hearing others thoughts and continuing the discussion!

Comments are closed.