December 7, 2025

Mallamai Na Ci Gaba Da Kira Ga Gwamnan Bauchi Game da Tsare Dr. Dutsen Tanshi

Al’umma na ci gaba da kira ga gwamnatin Bauchi da ta gabatar da shi a gaban kotu, ko a ba shi damar tattaunawa da Mallamai don a tabbatar masa da laifin da gwamnatin take zarginsa da shi ko kuma a sake shi.

Kira na baya bayan nan ya zo ne daga Sheikh Ahmad Tijjani, wanda shi ma ɗan jahar Bauchin ne. Shehin Mallamin ya bukaci gwamnati da ta yi wa Mallamin Musuluncin adalci.

Sheikh Guruntum ya yi zargin cewa siyasa ce ta sa ake ci gaba da tsare Mallamin wanda a baya ya sha fitowa fili yana nuna rashin goyon bayan dawowar gwamnatin Bala Mohammed a karo na biyu, da kuma marawa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023 da ya gabata.

Mallamin ya ƙara da cewa, “ko Fir’auna ya ba wa Annabi Musa damar tattaunawa da bokaye”.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shahararren Mallamin na ci gaba da zama a tsare ne sakamakon sharuɗɗan beli masu tsauri da kotun dake sauraron ƙararsa ta gindaya masa.

Sharaɗin shi ne, sai an samu Hakimi mai shaidar karatu ta digirin digirgir da zai tsaya masa.

This is the heading

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Ut elit tellus, luctus nec ullamcorper mattis, pulvinar dapibus leo.