Satar yara: Gwamnan Bauchi ya shawarci iyaye da su sanya ido kan ƴaƴansu

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya shawarci iyaye da kara sanya ido kan ƴaƴansu saboda gudun kar su faɗa mummunan hannu.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da iyayen yaran da aka sace da nufin yin fataucinsu zuwa kudancin Najeriya.
Ya ce, “Ɗazu na gana da jami’an gwamnati da iyayen ƴaƴan mu da aka sace aka canja musu suna tare da sayar da su inda aka yi yunƙurin fataucin su zuwa kudanci.”
Da yake yabawa gwamantin Kano game da ƙoƙarinta wajen ceto yaran, cewa ya yi, “Na fara da yabawa hoɓɓasar jami’an tsaro kan jajircewar su wajen ceto yaran da damƙe miyagun dake hannu kan wannan aika-aika, sannan na godewa gwamnati da al’umar jihar Kano kan tabbatar da nasarar haɗa waɗannan yara da iyayen su.”

Ya ƙara da cewa, “Wannan aiki abin yabawa ne matuƙa kuma ya dace da shirin gwamnatin mu na yaƙi da keta haddi, cin zarafi, bautarwa da kuma ayyukan assha tsakanin al’uma da tuni muka ƙirƙiri doka ta musamman don ladabtar da masu aikata hakan.
“Domin tabbatar da mayar da waɗannan yara makaranta da ba su ilimi don inganta rayuwar su, na bada gudummawar naira miliyan ɗaya ga iyayen kowane guda cikin su tare da jan hankalin da su kula tare da ƙara azamar ba su nagartacciyar tarbiya.
“Da wannan nake kira ga iyayen mu musamman mata da su ƙara sanya idanu kan hulɗa da zirga-zirgar ƴaƴan su, sannan malamai musamman na makarantin firamare, Islamiyyu da tsangaya da su samar da shirin kawo ko ɗaukar yara a makaranti.
“Mu kuma haɗa kai da sauran masu ruwa da jami’an tsaro ta hanyar ba su rahoton duk wani mutum, gungu ko ƙungiya dake barazana ga zamantakewa ko kyakkyawar mu’amala ko kuma yunƙurin musgunawa wani jinsi a cikin mu.”