Wata Baturiya ta haddace Alkur’ani a Kano
Daga Sabiu Abdullahi
Wata Baturiya ‘yar kasar Bulgaria Liliana Mohammed ‘yar kasar Bulgaria ta haddace Alkur’ani mai tsarki a jihar Kano.
Liliana ta zo Kano ne shekaru 32 da suka gabata, lokacin da aure ya kawo ta jihar tana da shekaru 30 da haihuwa.
Da take magana da manema labarai, Liliana ta bayyana cewa ta shigo Musulunci ne akalla shekara 10 da suka wuce.
Duk da shekarunta, Liliana ba ta ji ƙyuyar ta yi karatar littafi Mai Tsarkin ba, wanda malamarta, Malama Hafsa ta koya mata.