October 18, 2025

Sanata Natasha Akpoti Ta Zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, Da Yunkurin Lalata Da Ita

IMG-20250228-WA0007.jpg

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kokarin tilasta mata yin lalata da shi.

A wata hira da ta yi da Arise TV a ranar Juma’a, Akpoti ta ce matsalarta a majalisa ta fara ne tun bayan da ta ki amincewa da bukatar Akpabio.

“Na tsinci kaina a matsayin daliba da ake azabtarwa saboda ta ki yarda da bukatar malami na yin lalata da ita,” in ji ta.

A ranar 20 ga watan Fabrairu, sanatan ta yi musayar yawu da Akpabio a zauren majalisa bayan an sauya mata wurin zama, amma ta ki amincewa da hakan.

Akpoti ta bayyana cewa Akpabio ya yi kokarin nemanta ne a lokacin da ita da mijinta suka kai masa ziyara a Uyo, Jihar Akwa Ibom, don bikin zagayowar ranar haihuwarsa a watan Disamban 2023.

“Abin da ya faru a majalisa abu ne kawai da ya karade zuciyata. Amma matsalar ta fara tun a ranar 8 ga Disamba, 2023, a lokacin da muka je Uyo.

“Muna cikin gidansa ne a Ikot-Ekpene, daga nan muka tafi wani gida nasa a Uyo da misalin karfe takwas na dare. Ya kama hannuna yana nuna min gine-ginensa. Mijina yana biye da mu, yana duba wayarsa.

“A karshe sai ya ce ‘tun da yanzu kin zama sanata, zan ware lokaci domin mu dinga kwana a nan tare, za ki ji dadi sosai’. Nan take na fizge hannuna daga nasa,” in ji ta.

Ta bayyana cewa mijinta ya fahimci cewa wani abu ya faru, amma ta ki fada masa abin da Akpabio ya ce. Sai dai daga baya ya ja kunne cewa kada ta kara tafiya ita kadai ko zuwa gidan baƙi na Akpabio.

Haka kuma, sanatan ta kara da cewa a wani lokaci da ta je ofishin Akpabio domin jin dalilin da ya sa yake kin amincewa da kudirorinta, sai ya ce mata, “za ki more abubuwa da yawa idan har za ki kula da ni.”

Sai dai mai magana da yawun Akpabio, Eseme Eyiboh, bai mayar da martani ba kan wannan zargi, duk da kokarin da aka yi na tuntubarsa.