NSCDC Ta Kama Lita 1,571 Na Fetur Da Ake Zargin Za A Kai Wa ‘Yan Bindiga a Zamfara

Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta kama lita 1,571 na man fetur da aka yi fasa ƙwaurinsu, ana zargin ana shirin kai su ga ‘yan bindiga a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na NSCDC a jihar, Sani Mustapha, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin kwamandan rundunar, ya bayyana cewa an kama mutane huɗu da ake zargi da aikata laifin a wurare daban-daban.
Biyu daga cikin waɗanda aka kama ma’aikatan wani gidan mai ne, yayin da aka cafke sauran biyun a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe.
A cewar Mustapha, ba wai kawai an kama su da fetur ɗin da aka yi safara zuwa wuraren da ba a yarda da su ba, har ma sun karya dokar da gwamnan jihar ya sanya wa hannu, wacce ta hana sayar da fetur a jarka.
Ya ce an kama biyu daga cikinsu a Birnin Magaji da lita 1,296, yayin da aka kama sauran biyun a Tsafe da lita 275.
“A yau mun gabatar muku da waɗanda ake zargi da safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan ya saɓa dokokin ƙasa da na jiha, musamman hana sayar da fetur a jarka,” in ji shi.