Nuhu Ribadu Ya Musanta Zargin El-Rufai Kan Biyan Kuɗin Fansa Ga ’Yan Bindiga

Daga TCR HAUSA
Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) ya musanta zargin da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi cewa gwamnati na biyan kuɗi da kuma ba wa ’yan bindiga wasu abubuwa domin samun zaman lafiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin, Zakari Mijinyawa, ya fitar a daren Lahadi, ya bayyana cewa wannan zargi ba shi da tushe.
“Babu wani lokaci da ONSA ko wata hukuma a ƙarƙashin wannan gwamnatin ta shiga harkar biyan fansa ko bayar da tallafi ga masu laifi. Akasin haka, mun sha gargadin ’yan Najeriya da kada su biya fansa. Zargin El-Rufai ƙarya ne kuma ya saba wa hujjojin da ake iya gani a kasa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa tun daga farko, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauki dabaru biyu a lokaci guda: gudanar da ayyukan soji da ƙarfin iko tare da tattaunawa da al’umma domin magance ƙorafe-ƙorafen cikin gida.
Ofishin da Nuhu Ribadu ke jagoranta ya ce wannan tsari ya kawo sauƙi a wasu sassa na Jihar Kaduna kamar Igabi, Birnin Gwari, da Giwa, waɗanda suka sha fama da hare-haren ta’addanci a baya, amma yanzu suna samun ɗan kwanciyar hankali.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa an samu nasarori wajen kawar da manyan shugabannin ’yan bindiga a jihar. A cewar ONSA, a Kaduna kaɗai an hallaka ko kuma an kama shahararrun masu ta’addanci kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka, tare da cafke shugabannin kungiyar Ansaru da suka kafa sansanoni a yankin.
Sai dai ONSA ta bayyana cewa wannan nasara ta zo da asara, domin wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu a yayin fafatawa.
“Don tsohon gwamna irin El-Rufai ya ƙaryata waɗannan sadaukarwa a kafar talabijin ta ƙasa, abin takaici ne kuma cin mutunci ga tunawa da jami’an tsaronmu,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, “muna kira ga El-Rufai da sauran ’yan siyasa da su guji ja da hukumomin tsaro cikin rikicin siyasa. Yaƙi da ’yan bindiga aiki ne na haɗin kai, ba dandalin neman maki na siyasa ba ne.”