January 15, 2025

Da makamai mallakin gwamnati ake amfani wajen aikata laifuka a Najeriya, cewar NSA Nuhu Ribadu

3
FB_IMG_1729190456410.jpg

Daga Sabiu Abdullah


Mai ba da shawara kan tsaron kasa na Najeriya, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa, yawancin makaman da ake amfani da su wajen aikata laifuka a kasar asali na gwamnati ne.

Ribadu ya yi wannan jawabin ne yayin wani taron lalata makamai da Cibiyar Kasa mai kula da Haramtattun Makamai da Manyan Bindigogi ta shirya.

“Mutum mafi muni shi ne dan sanda ko soja wanda zai dauki makamai daga wurin aikinsa ya sayar ko ya ba da hayar su ga miyagu don su kashe abokan aikinsa,” in ji Ribadu, yana la’antar jami’an tsaro da ke taimaka wa ‘yan ta’adda da wasu da ba na gwamnati ba wajen samun makamai.

Taron ya yi niyyar lalata sama da makamai 2,400 da suka hada da wadanda ba sa aiki, wadanda aka cire daga aiki, da kuma wadanda aka kwato.

Shugaban cibiyar, Johnson Kokumo, ya bayyana cewa wannan yunkuri zai rage hadari ga al’umma, tare da isar da sakon gargadi game da fataucin makamai na haram.

3 thoughts on “Da makamai mallakin gwamnati ake amfani wajen aikata laifuka a Najeriya, cewar NSA Nuhu Ribadu

  1. Keep up the fantastic work! Kalorifer Sobası odun, kömür, pelet gibi yakıtlarla çalışan ve ısıtma işlevi gören bir soba türüdür. Kalorifer Sobası içindeki yakıtın yanmasıyla oluşan ısıyı doğrudan çevresine yayar ve aynı zamanda suyun ısınmasını sağlar.

  2. This is very interesting, You are a very skilled
    blogger. I have joined your feed and look forward to seeking more of
    your fantastic post. Also, I’ve shared your site in my social networks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *