Ba ruwana a dambarwar sarautar Kano, inji Nuhu Ribadu
Daga Abdullahi I. Adam
Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalm ya zargi mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da haddasa badaƙalar komar da Alhaji Aminu Ado Bayero Kano don ci gaba da sarauta.
A wani faifan bidiyo da gidan rediyon Freedom Kano ya saki, an jiyo mataimakin gwamnan na nanata cewa abinda Aminu Ado ya aikita ba daidai ba ne kuma tabbas za su ɗauki mataki.
A zargin da mataimakin gwamnan ya yi an jiyo shi yana cewa ”mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ne ya bayar da jirage guda biyu domin ɗauko tsohon sarki domin su kawo shi Kano,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Mal. Nuhu Ribadu ya musanta zargin inda mai magana da yawun mashawarcin Shugaban Ƙasan, Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa babu hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a komawar tsohon sarkin.
Mijinyawan ya ƙara da cewa zargin na mataimakin gwamnan na Kano ”ba gaskiya ba ne, babu wanda ya bayar da jirgi domin mayar da shi, saboda wannan ba aikinmu ba ne,” kamar yadda ya ambata.
Mijinyawan ya ƙara da cewa ”babu wani jami’in tsaro da muka tura Kano, ai suma suna da jami’an tsaro, ai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gabatar da taron manema labarai, kuma kowa ya ji yana cewa aikinsa yake yi, ba wanda ya saka shi.”
A halin da ake ciki, birnin na Kano na cike da jami’an tsaro wanda kuma ɗazu-ɗazunnan aka jiyo su suna faɗan cewa ba za su bari a keta doka da oda ba kan wannan lamari na sarauta a faɗin jihar, kamar yadda Kwamishinan ‘Yan sanda na Kanon CP Mohammed Usaini Gumel ya faɗa ma manema labaru a wata sanarwa.