October 18, 2025

NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Ƙin Ƙaddamar Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

FB_IMG_1731322542266.jpg

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta ba da umarnin shiga yajin aiki ga ma’aikatan jihohin da ba su aiwatar da sabon ƙaramar albashi ba daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

Wannan umarni ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, ya fitar bayan taron majalisar zartarwa na ƙungiyar a Fatakwal.

Sanarwar ta nuna rashin gamsuwar ƙungiyar da jinkirin da wasu jihohi ke yi wajen aiwatar da sabon tsarin na 2024, inda ta bayyana hakan da cewa ya saɓa doka kuma yana nuna rashin adalci.

Ajaero ya yi nuni da cewa ƙin aiwatar da tsarin ya ƙara ta’azzara wahalar rayuwar ma’aikata a Najeriya, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ke ƙara hauhawa.

NLC ta lashi takobin daukar matakan gaggawa da suka haɗa da yajin aiki idan gwamnatocin jihohin ba su bi wannan sabon tsari ba kafin farkon watan Disamba, tare da kira ga gwamnatocin jihohin da su nuna tausayi ga ma’aikata.

15 thoughts on “NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Ƙin Ƙaddamar Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

  1. Do yoou have a spa prolblem onn tbis blog; I aloso aam a blogger,
    andd I was wantiing tto kbow ykur situation; many of
    us have created some nice msthods andd we are looking to trade solutioons witth otuer
    folks, please shot mme ann e-mail if interested.

  2. I got tbis site from myy friend wwho informedd me copncerning thus web site and now thios time I aam visiting thios ebsite and reading very
    informative posts at this time.

Comments are closed.