January 24, 2025

Najeriya Ta Sake Jaddada Goyon Bayan Tsagaita Wuta a Yakin Isra’ila da Gaza

0
FB_IMG_1731351173826.jpg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Ministan Labaru na Najeriya, Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Najeriya na ganin an sami maslaha cikin lumana a rikicin Isra’ila da Falasɗinu.
 
A yayin taron hadin gwiwa na Larabawa da Musulmi da ake gudanarwa a Riyadh, Saudiya, ana sa ran Shugaba Tinubu zai sake kiran Najeriya na neman a samu tsagaita wuta da warware rikicin.
 
A cewar Idris, halartar Najeriya a taron ya dogara ne da dadadden dangantakar da ke tsakaninta da yankin Gabas ta Tsakiya.
 
Ya jaddada cewa rikicin ba zai taba samun mafita ta hanyar yaƙi ba, yana mai cewa, “Dole mu nemi mafita ta diflomasiyya, kuma wannan ne dalilin zuwanmu nan.”
 
Najeriya tana marawa tsarin maslahar “kasashen biyu” baya a matsayin mafita, inda take ganin Isra’ila da Falasɗinu za su iya rayuwa tare cikin zaman lafiya da kimanta juna.
 
Kasar dai ta amince da kasancewar Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta tun 1988, kuma tana goyon bayanta a Majalisar Dinkin Duniya.
 
Rikicin ya haifar da ra’ayoyi daban-daban a fadin Afirka, inda wasu kasashen ke goyon bayan Isra’ila, wasu kuma na goyon bayan Falasɗinu.
 
Aljeriya, Tunisiya, Afirka ta Kudu, da Sudan sun nuna goyon baya ga Falasɗinu, yayin da Kenya, Ghana, Rwanda, da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo suka nuna goyon baya ga Isra’ila.
 
Matsayar Najeriya kan rikicin ya nuna yadda take kallon Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta da kuma jajircewarta kan zaman lafiya.
 
Yayinda taron na Hadin Kan Larabawa da Musulmi ke ci gaba, ana sa ran muryar Najeriya za ta taka rawar gani wajen tsara martanin al’umma dangane da rikicin.
 
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *