NCC ta ce a rufe duk layukan salular da ba a hada su da NIN ba

Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar NCC wacce ke kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta sake jaddata umarninta ga kamfanonin sadarwar na da su toshe duka layukan wayar da ba a haɗa su da lambar katin ɗa ƙasa, wadda aka fi sani da NIN, ba.
Reuben Mouka, daraktan yaɗa labarai na hukumar, ne ya sanar da wannan umarnin.
Mouka ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron kasuwanci da aka gudanar a birnin Kaduna.
Mista Mouka ya ce dole ne masu amfani da layin waya su haɗa shi da lambar katin ɗan ƙasarsu ta NIN, yana mai cewa an ɗauki matakin ne don magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Ya ƙara da cewa yau Laraba aka ba wa kamfanonin sadarwar su rufe duka layukan da ba a haɗa da lambar NIN ba.