Matashi ya yi tattaki tun daga Gombe har zuwa Abuja domin karrama shugaban soji
Daga Sabiu Abdullahi
Wani direban mota mai shekaru 21 daga jihar Gombe, Suleiman Rabiu, ya yi wani tattaki na ban-mamaki, inda ya yi tafiya ta sama da kilomita 700 domin nuna jin dadinsa da halayen shugaban rundunar sojojin kasa (CDS), Janar Christopher Musa.

Rabiu ya tashi daga jihar Gombe ne a ranar 12 ga watan Fabrairu ya isa Abuja a ranar 28 ga Fabrairu, 2024, inda ya kwashe tsawon kwanaki 16 a kan hanya.
A cewar sanarwar da Daraktan yada labarai na tsaro, Brig. Janar Tukur Gusau, ya fitar, Rabi’u ya samu kwarin guiwar salon jagorancin Janar Musa, wanda a ganinsa ya inganta harkar tsaro sosai a kasar nan.
Sanarwar ta kara da cewa “Suleiman, wanda ya fara wannan tafiya duk da yanayi marar kyau, ya yi niyyar nuna jin dadinsa ga kyawawan halayen jagoranci na shugaban sojin ne”
Rabiu ya bayyana irin ci gaban da aka samu a harkar tsaro tun bayan hawan Janar Musa, inda ya danganta hakan ga ingantaccen jagoranci a cikin rundunar sojin kasar.




