October 18, 2025

Muna nan daram a bayan Falasɗinu—Yariman Saudiyya

Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya faɗa wa Shugaban Falasɗinu Mahmud Abbas cewa Masarautar Saudiyya za ta ci gaba da “taimaka wa al’ummar Palasdinu don cimma halattancen ‘yancinsu na rayuwa mai kyau, da cim ma burinsu, da samun zaman lafiya mai dorewa,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ambato shi.

Yariman na Saudiyya ya kuma shaida wa Shugaba Abbas cewa yana bakin ƙoƙarinsa don hana “faɗaɗuwar” rikici bayan harin ba-zata da Hamas ta kai kan Isra’ila.

Sakamakon hare-haren da kungiyar Islama ta Falasɗinawa ke kaiwa a kasa da sama da kuma ta ruwa ba a taba yin irinsa ba, Isra’ila ta ƙirga mutane 800 tare da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 687.

263 thoughts on “Muna nan daram a bayan Falasɗinu—Yariman Saudiyya

  1. психоневрологический дом интернат для престарелых и инвалидов [url=https://xn—-1-6cdshu4albf3aye.xn--p1ai]https://xn—-1-6cdshu4albf3aye.xn--p1ai[/url] .

Comments are closed.