January 14, 2025

Shugaban Najeriya Tinubu zai halarci muhimmin taron tattalin arziki a Riyadh

0
images-2023-11-06T060936.025.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

A kokarin inganta Najeriya da kuma jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye daga ƙetare, Shugaba Bola Tinubu na shirin tafiya birnin Riyadh na kasar Saudiyya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Tafiyar dai ta zo daidai ne da taron ƙolin Saudiyya da Afirka da kuma taron ƙasashen Larabawa da Afirka da aka shirya gudanarwa a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamba, 2023, bi-da-bi.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya yi wa manema labarai ƙarin haske a fadar shugaban kasa, inda ya jaddada manufofin shugaban a yayin ziyarar tasa.

Tinubu, wanda kuma ke rike da muƙamin shugaban hukumar gudanarwar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), zai taka rawar gani a taron.

Muhimman abubuwan da ya mayar da hankali a kai sun hada da tattaunawa kan alaƙar tattalin arziki tsakanin yankunan, ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci, matsalolin muhalli, da noma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *