Matsalar Arewa Ita ce Jagororin Yankin, Cewar Yakubu Dogara

Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa koma-baya da ake fuskanta a yankin Arewa ya samo asali ne daga jagorancin shugabannin siyasar yankin.
Dogara ya yi wannan jawabin ne a wani taron jagororin Kiristoci daga arewacin Najeriya, inda ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, musamman kan tsare-tsarensa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ta hanyar sabbin ƙudurorin haraji.
A cewarsa, shugabannin Arewa ba su amfana da kusan shekaru 40 na ikon siyasa domin ci gaban yankin, wanda hakan ya haifar da yawaitar talauci da rashin aikin yi.
“Ba Tinubu ko yankin kudu ba ne matsalarmu. Wasu na ƙorafin cewa Yarbawa suna samun muƙamai da yawa, amma kar mu manta, mun yi mulkin sama da shekara 40. Me za mu nuna? Har yanzu Arewa na nan yadda take,” in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dogara ya kuma yi kira ga shugabannin yankin su yi nazari kan irin rawar da suka taka domin ganin an magance matsalolin da ke ci gaba da durƙusar da Arewa.