October 18, 2025

Masanin adabi Soyinka ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa masu zanga-zanga da ‘yan jarida

images (6) (29)

Daga Sabiu Abdullahi  

Fitaccen marubucin nan na adabi, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kakkausar suka ga hare-haren da jami’an tsaro ke kaiwa masu zanga-zangar #EndBadGovernanceInNigeria da ‘yan jarida, yana mai bayyana amfani da harsasai da hayaki mai sa hawaye a matsayin “koma baya” da zai haifar da tashin hankali.  

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, Soyinka ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin tarayya ke daukar da zanga-zanga, inda ya ce amfani da harsashi na gaskiya da hayaki mai sa hawaye da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi ba zai haifar da da mai ido ba.  

Ya bukaci hukumomin tsaro da su yi amfani da wasu hanyoyi na magance zanga-zangar jama’a da kuma guje wa munanan hanyoyin tarwatsa masu zanga-zangar, inda ya ba da misali da yunkurin 2022/23 YELLOW VEST a Faransa, inda hukumomin tsaro ba su yi amfani da bindigogi kan masu zanga-zangar ba.  

Soyinka ya kuma yi kira ga gwamnati da ta daina “muguwar dabi’a” ta mayar da martani da ƙarfi a kan mutane, yana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata a yi watsi da wannan shirin don komawa zuwa ga nagartattun hanyoyi na dindindin.

3 thoughts on “Masanin adabi Soyinka ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa masu zanga-zanga da ‘yan jarida

  1. I will immediately grab your rss as I can’t to find your email subscription link or newsletter service. Do you have any? Kindly allow me understand so that I may just subscribe. Thanks.

Comments are closed.