October 18, 2025

Kuna da labarin mutumin da aka hallaka masa ƴan’uwa guda 103 a Gaza?

image_editor_output_image-233966193-1709094055335.jpg

—Wallafar BBC Hausa

Ahmad al-Ghuferi ya tsira daga bam ɗin da ya kawar da iyalansa daga duniya.

Lokacin da wani hari ya hallaka iyalai da ƴan’uwansa su 103 a gidansu da ke Gaza, yana can maƙale a garin Jericho na Gaɓar Yamma, kimanin kilomita 80 daga gida.

Ahmad na aiki ne a wani wurin da ake aikin gini a Tel Aviv, lokacin da Hamas ta kai hari cikin Isra’ila a ranar bakwai ga watan Oktoba – ya kasa komawa gida wurin matarsa da ƴaƴansa mata uku sanadiyyar yaƙin da ya ɓarke da kuma rufe hanyar da sojojin Isra’ila suka yi.



A kullum akwai lokacin da suka ware shi da iyalansa domin yin waya da juna idan layin yana da kyau, kuma ko a lokacin da aka kai harin, yana kan waya tare da matarsa Shireen a ranar takwas ga watan Disamba.

Ya ce “Kamar ta san cewa za ta mutu, ta ce min na yafe mata kan duk wani abu maras kyau da ta taɓa yi min. Na ce mata ta daina irin wannan maganar. Amma wannan ce waya ta ƙarshe tsakaninmu.”

Wani mummunan harin bam da aka kai a gidan kawunsa a yammacin ranar ne ya hallaka matarsa da ƴaƴansa mata uku – Tala da Lana da kuma Najla.

Haka nan harin ya kashe mahaifiyar Ahmad, da ƴan’uwansa maza huɗu da iyalansu, da ƴan’uwan mahaifiyarsa da sauran dangi, su sama da 100.

Wata biyu bayan mummunan harin har yanzu gawawwakin wasu daga cikin su na maƙale a ƙarkashin gini.

A makon da ya gabata ne ya kamata ƴar’autarsa, Najla ta cika shekara biyu da haihuwa. Har yanzu Ahmad na fama da jimamin rashin iyalansa.

Kasancewar ba ya nan a lokacin da suka rasu da kuma lokacin da aka binne su, har yanzu Ahmad idan yana magana sai ya riƙa yi tamkar iyalan nasa na da rai, a wasu lokutan hawaye na kwarara daga idanunsa.

“Ƴaƴana su ne farin cikin raina,” in ji shi. “Ji nake kamar a mafarki. Har yanzu na kasa yarda cewa wannan lamarin ya faru.”

Ya goge hotunansu da ke wayarsa da komfutar tafi da gidanka saboda ka da abin da rinka damun sa.

An bar shi da haɗa labarin abun da ya faru daga abubuwan da makwabta da ƴan uwan da suka yi saura suka gaya masa.

Sun shaida masa cewa an harba makami mai linzami ne a ƙofar shiga gidan da iyalan nasa suke.

“Sun ruga da gudu suka shiga gidan wani kawuna da ke kusa, bayan mintoci 15 kuma sai wani jirgin yaƙi ya zo ya jefa bam a gidan. ” Ahmad ya bayyana.

Ginin mai hawa hudu da aka kashe iyalan nasa na kusa da wata kwana daga cibiyar lafiya ta Sahaba a birnin Zeitoun da ke Gaza.

Abun da ya rage yanzu sai tudun ƙasa da baraguzai da launin jini nan da can da yagaggun tufafi da kura ta buɗe.