Hamas ta sake sakin fursunoni biyu
Daga Usama Taheer Maheer
Ƙungiyar Hamas ta bayyana cewa ta sake sakin fursunoni biyu acikin fursunonin da ta yi garkuwa da su yayin harin da ta kai a Isra’ila, wanda ya haddasa kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a yankin Falasɗinu yanzu haka.
Rahotanni na nuni da cewa akwai yiwuwar ƙara sakin fursunoni 50 nan gaba sakamakon tattaunawar sasanci wadda ƙasar Qatar da Egypt su ke jagoranta.
Ranar Juma’ar da ta gabata Hamas ta saki fursunoni ƴan asalin ƙasar Amurka guda biyu, Natalie da Judith Ranaan.
Har yanzu babu cikakken bayani game da sunayen waɗan da kungiyar ta bayyana sakin nasu a wannan karon.