Kotu ta tabbatar da zaɓen gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri

Daga Sabiu Abdullahi
Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Adamawa.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan taƙaddamar shari’a da Aisha ‘Binani’ Dahiru ta jam’iyyar APC da wasu ’yan takara suka fara, wadanda suka nemi ƙalubalantar nasarar Fintiri.
Hukuncin kotun ya tabbatar da matsayin Fintiri a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen, tare da tabbatar da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana tun farko.
Tun farko dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 430,861, inda ya zarce ‘yar takararsa Aisha ‘Binani’ Dahiru wadda ta samu kuri’u 398,738.
Rashin gamsuwa da sakamakon zaben ya sa Mrs Dahiru da wasu ‘yan takara da dama suka tunkari kotun inda suka nuna shakku kan sahihancin nasarar da Fintiri ya samu.
Hukuncin kotun a yanzu ya tabbatar da sahihancin nasarar Fintiri, wanda ya kawo karshen kalubalen shari’a da ya dabaibaye zaben gwamnan jihar ta Adamawa.