October 18, 2025

Koriya ta Arewa da Rasha Sun Ƙulla Yarjejeniya Don Ƙarfafa Hadin Gwiwar Soji

images-57.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Koriya ta Arewa ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwar dabarun soja tare da Rasha, wanda zai ƙarfafa haɗin gwiwar soja a tsakaninsu.
 
A cewar kamfanin dillancin labarai na gwamnati a Pyongyang, KCNA, an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Litinin, kuma za ta fara aiki bayan musayar takardun amincewa daga bangarorin biyu.
 
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sanya hannu a kan yarjejeniyar a ranar Asabar, bayan da majalisar dokokin ƙasa ta Rasha ta Duma ta amince da ita a ranar 24 ga Oktoba.
 
Yarjejeniyar ta tanadi taimakon juna idan aka kai hari, kuma tana nuna babban ci gaba a haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu.
 
Wannan ci gaban ya zo ne a yayin da ake rahoton cewa sojojin Koriya ta Arewa suna yaƙi tare da Rasha a kan Ukraine.