January 24, 2025

Shugaba Putin na shirin sauke ministan tsaron Rasha

6
IMG-20240513-WA0005.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin na shirin sauke daɗaɗɗen abokinsa Sergei Shoigu daga muƙamin ministan tsaron ƙasar.

Kamfanonin dillancin labaran ƙasar, sun ce shugaba Putin na shirin naɗa mista Sergei Shoigu shugaban majalisar tsaron ƙasar.

Sergei Shoigu, mai shekara 68 ya shafe shekara 12 yana riƙe da muƙamin minista a ƙasar.

Wasu takardu da majalisar dokokin ƙasar ta wallafa sun ce Andrei Belousov ne zai maye gurbin ministan tsaron.

Mista Shoigu ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin da Rasha take yi a Ukraine.

Wasu bayanai daga gwamnatin Rasha na nuna cewa shugaba Putin na son mista Shoigu ya karɓe ragamar majalisar tsaron ƙasar daga hannun Nikolai Patrushev.

6 thoughts on “Shugaba Putin na shirin sauke ministan tsaron Rasha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *