October 18, 2025

Kisan al’ummar annabi: kuskure ko ganganci

FB_IMG_1701756740409.jpg

Daga Malam Salihu Sule Khalid

Hakika ‘kuskuren’ da aka yi wanda ya hallaka rayukan mutane masu gudanar da mauludi a Kaduna ya ƙara bayyana sakaci ko ka ce ganganci a yadda ake gudanar da ayyuka a ƙasar nan. Musamman ayyukan da suka shafi kare lafiya da dukiyar al’umma.

Wannan ba wai kware baya ne ga jami’an tsaro ba. Makamancin haka ya faru sau adadin da bai cancanci ai uzuri a kau da kai ba. Nauyi ya rataya a kan mahukunta da su duba lamarin nan cikin gaggawa kuma a bi wa masu haƙƙi haƙƙinsu. Sannan kuma a ɗauki ƙwararan matakai don gujewa maimai. Tabbatuwa da nasarar hakan kuma zai ta’allaƙa ne da irin muhimmancin da muka ba wa abin a matsayinmu na ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da kowane bambanci ba.

Muna fatan Allah Ya jikan wadanda suka rasa rayukansu. Wadanda suka ji rauni Allah Ya ba su lafiya.

87 thoughts on “Kisan al’ummar annabi: kuskure ko ganganci

  1. Great site with quality based content. You’ve done a remarkable job in discussing. Check out my website QN9 about Airport Transfer and I look forward to seeing more of your great posts.

Comments are closed.