October 18, 2025

Jita-jitar rashin lafiyar Tinubu: Wane halin shugaban yake ciki?

image_editor_output_image319321887-1728625420630.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Jita-jita ta yadu a kafafen sada zumunta cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga wani hali na rashin lafiya mai tsanani, wanda ake zargin ya sa aka yi masa gaggawar kai shi asibiti a birnin Landan.

Wasu daga cikin masu yada wannan labari sun fara yin murnar rashin lafiyar shugaban kasar, har ma wasu na cewa ya rasu.

Wadannan kalamai sun samo asali ne daga yadda wasu ‘yan Najeriya ke danganta matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta da manufofin gwamnati, wadanda suka ce sun kawo musu wahala mai tsanani.

Duk da haka, ba a sami wani tabbaci daga bangaren gwamnati ba game da wadannan jita-jita.

Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga ofishin shugaban kasa ko wani jami’in gwamnati da ke tabbatar da sahihancin wannan labari.

Jaridar The Citizen Reports ta yi kokarin tuntubar Bayo Onanuga, Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai, domin jin gaskiyar lamarin, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba mu samu amsa daga gare shi ba.

Masu sa ido na ci gaba da jira don jin sahihin bayani daga hukumomin gwamnati game da halin da shugaban kasa ke ciki.

Za mu ci gaba da kawo muku cikakkun bayanai yayin da lamarin ke ci gaba da gudana.