October 18, 2025

#ImoKogi: Shugaban APC Ganduje ya taya Ododo da Uzodinma murnar lashe zaɓe

images-2023-11-13T071056.689.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta kasa, Abdullahi Ganduje, ya taya Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo murnar sake samun nasara a zaben gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.

Mista Ganduje ya kuma nuna farin cikinsa da goyon bayan da masu zabe a jihar Kogi suka nuna na Ahmed Ododo a zaben gwamnan jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Edwin Olofu, ya fitar, ya bayyana cewa zaɓukan Uzodimma da Ododo sun nuna cewa ‘yan Najeriya na tare da APC.

Mista Ganduje ya kuma ce nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihohin biyu na nuna yadda ‘yan kasa ke yaba wa yadda Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da kuma gwamnan jihar Kogi mai barin gado, Yahaya Bello, suka gudanar da dimokuradiyya.

62 thoughts on “#ImoKogi: Shugaban APC Ganduje ya taya Ododo da Uzodinma murnar lashe zaɓe

Comments are closed.