May 13, 2025

Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya

IMG-20231112-WA0014-750x819.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wata motar bas da ke ɗauke da jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta gamu da wani mummunan haɗari, wanda ya yi sanadin asarar rayuka.

Hukumar kiyaye haddura ta tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane biyu nan take, yayin da wasu bakwai da suka jikkata aka kai su asibiti ba tare da ɓata lokaci ba.

Jami’an, waɗanda suka dawo Abuja daga jihar Kano bayan faretin gama horarwa a makarantar horas da shige da fice, sun yi hatsarin ne a hanyar Kano zuwa Zariya.

Har yanzu dai ba a san ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, amma rahotanni na nuni da cewa wata kila fashewar tayar ne ya janyo haɗarin.