October 18, 2025

Gwamnatin Najeriya ta yi afuwa wa fursunoni a Kano

images-2023-12-01T105325.492.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin tarayya ta yi wa fursunoni guda 150 afuwa a jihar Kano

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da sakin.

A cewarsa manufar wannan ƙudiri an yi shi ne don samar da yanayi mai kyau na mutuntaka a gidajen gyaran hali.

Baya ga haka, ya sanar cewa an tara naira biliyan 585 ta hanyar ayyukan agaji, inda aka ware naira biliyan 13,436,780.00 ga Jihar Kano.

Babban Alkalin Jihar Gombe Ya Saki Fursunoni 182

A daya bangaren kuma, Mai shari’a Halima Sadiya Mohammed, babbar mai shari’a ta jihar Gombe, ta bayar da gudunmawar sakin fursunoni 182 daga cibiyoyin da ake tsare da su a ƙarƙashin rundunar jami’an kula da gidajen gyaran hali na jihar Gombe.

Daga cikin jimillar fursunoni 141 an saki fursunoni 141 daga cibiyar gyaran hali na ƙaramar hukumar Gombe.

Kwanturolan hukumar NCoS reshen jihar Gombe Lawan Idris Gusau ya yaba wa babbar alkaliyar da kwamitin bisa ƙoƙarinsu.