October 18, 2025

Gwamnan Bauchi ya biya wa maniyyata cikon kuɗaɗen aikin Hajji

images-1-16.jpeg


Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ta biya rabin cikon kuɗaɗen da hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta buƙaci dukkanin maniyyata su biya.

Lawal Muazu Bauchi, mai tallafa wa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a yau Juma’a.

Wannan kuɗi dai ya kai kimanin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara da kwabbai.

Ainihi dai sanarwar ta fito ne daga babban sakataren hukumar kula fa jin daɗin alhazai ta jihar Bauchi, Imam Abdurrahman.

Ya ce gwamna Bala ya biya kaso hamsin (50%) ga kowane maniyyaci, wato kimanin naira dubu ɗari tara da hamsin ke nan.

Sanarwar Lawan ta ci gaba da cewa, “Sanya tallafin na cikin shirin gwamnatin Sanata Bala Muhammad na sauƙaƙa rayuwa da kuma tabbatar da walwalar maniyyata anan gida Najeriya dama ƙasa me tsarki yayin sauƙe farali.


“Hukumar jin daɗin alhazan sai tayi amfani da sanarwar don yabawa me girma gwamna kan tallafin da kuma sauran ayyukan jin-ƙai da gwamnatinsa ke yi don daɗaɗawa maniyyata, tare da yi masa addu’ar fatan nasara.“