January 14, 2025

Gwamna Bala zai ba wa ma’aikatan jiharsa tallafin naira dubu goma-goma

0
image_editor_output_image371360463-1718470327406.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya umurci a biya kowane ma’aikacin jihar tallafin naira dubu goma-goma don yin hidimar sallah.

Kamar yadda ya bayyana a yau ɗin nan a shafinsa na Facebook, Gwamna Bala ya ce “lura da halin ƙuncin da tsadar rayuwa da muka tsinci kanmu a ciki a wannan lokaci da muke shirin bikin Babbar Sallah, na amince da biyan tallafin dubu goma-goma ga ɗaukacin ma’aikata a jihar mu ta Bauchi, a wani matakin rage raɗaɗi.”

Haka nan kuma, gwamnan ya ƙara da cewa “ba za mu gajiya ba wajen kira ga al’umma da su sanya jihar Bauchi da kuma ƙasarmu Najeriya cikin addu’o’insu don samun bunƙasar zaman lafiya da haɓakar tattalin arziki, musamman a wannan ranaku masu ɗimbin albarka.”

Daga ƙarshe gwamnan ya nemi al’umma da su tallafa wa mabuƙata da marasa lafiya gami da masu ƙaramin ƙarfi a wannan lokaci na bukukuwan sallah tare da roƙon Allah Ya amshi ibadun da ake aikatawa a wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *