October 18, 2025

Gwamna Bala ya rattaɓa hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2024

images-2023-12-29T120745.043.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2024.

Mai taimaka wa gwamnan ta fuskar yada labarai na zamani, Lawal Muazu Bauchi, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.

A cewar Lawal, gwamnatin ta yi shirin “yaƙi da talauci da inganta ilimi, lafiya da kuma hanyoyi a yankunan karkara da birane.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Da yake jawabi yayi bikin sanya hannun da ya gudana a fadar gwamnati a gaban kakakin majalisar dokokin jiha da manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi, Bala Muhammad yace kasafin da ya ƙunshi sama da naira biliyan ɗari uku zai ɗora kan ayyukan waɗanda suka gabace shi na gina ɗakunan karatu a makarantin gwamnati, kwaskwarima wa manyan asibitoci tare da gina ƙanana a duk faɗin jiha.

”Gwamnan yace sashen ilimi zai laƙume naira biliyan goma sha biyar, kaso me tsoka kamar yadda ya bayyana yayin taron inganta ilimi kuma wani matakin cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa.

“Sai ya yabawa shugabancin majalisar dokoki kan goyon baya da haɗin kai da take bada fannin zartaswa inda ya ƙudiri aniyar ruɓanya shirin gwamnatin sa na damawa da kowa musamman mata da matasa da ya bayyana su a matsayin ƙashin bayan kowace al’uma.

“Bala Muhammad sai ya godewa sarakuna da masarautun gargajiya, malaman addini da kuma ƙungiyoyi kan goyon bayan su ga jami’an tsaro a yaƙi da miyagu da ɓata-gari.”