Gobara ta kama Gidan Gwamnatin Jihar Katsina

Daga Sabiu Abdullahi
Gobara ta tashi a ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Katsina da ke Katsina, inda ta kone wani bangare na ginin.
Wurin da abin ya shafa na manne da ofishin da Gwamnan ke ganawa da wasu muhimman mutane.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar da barnar da ta yi ba.
Ana ci gaba da kokarin kashe gobarar da hana ci gaba da yaɗuwa.
Kawo yanzu dai babu wani karin bayani dangane da lamarin, kuma har yanzu jami’ai ba su ce komai kan lamarin ba.
Ana sa ran bincike kan gobarar zai bayyana karin bayani kan musabbabinta da tasirinta.