Gwamnatin Katsina ta ware naira biliyan 30 domin ganin bayan matsalar tsaro
Daga Abdullahi I. Adam
Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Danmusa, ya ce gwamnatin jihar ta ware sama da ₦30bn domin yaƙi da rashin tsaro a faɗin jihar.
Kwamishinan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, ya bayyana cewa ware waɗannan maƙudan kuɗaɗe na daga cikin jajircewar Gwamna Dikko Radda na yaƙi da rashin tsaro da kuma maido da dawwamammen zaman lafiya a faɗin jihar
A cewar kwamishinan, an ware kuɗaɗen ne domin baiwa jami’an tsaro kayan aiki, da inganta ayyukan leƙen asiri, da kuma tallafawa ayyukan da suka shafi al’umma da nufin hana aikata laifuka.
Haka nan kuma kwamishinan ya bayyana wasu cewa matakan da ake ɗauka a jihar suna haifar da sakamako mai kyau, tare da raguwar ta’annatin ayyukan ‘yan fashi da sauran ayyukan laifi.
“Ƙudirin gwamnati ne na ci gaba da ba da fifiko kan tsaro da jin daɗin ‘yan ƙasa. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za a tsagaita ba wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar Katsina har sai mun ci nasara.
“Kamar yadda ba a taɓa yin irinsa ba, ina ƙara jaddada cewa gwamnatin jihar ta sake sabunta alkawarinta na yaƙi da rashin tsaro har sai ya tsaya cak.
“Haƙƙinmu gaba ɗaya, kuma dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu tashi tsaye don kawar da rashin tsaro a Katsina,” inji kwamishinan.