October 18, 2025

Babu wani shirin kawo hari jami’ar Abuja—Ƴansanda

IMG-20240910-WA0013

Daga Sodiqat A’isha Umar

Rudunar ƴansandan Najeriya ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa na zargin shirya garkuwa da mutane a jami’ar Abuja.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ƙasar nan, ke shirin gudanar da bukukuwan cika shekara 64 da samun ‘yancin kai cikin mako mai zuwa.

A ‘yan ƙwanakin nan ne dai zargin shirya garkuwa da mutane a jami’ar ya karaɗe shafukan sada zumunta.

To sai dai cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan birnin Abuja, Josephine Adeh ta fitar ta ce rahotonnin shirya harin ba gaskiya ba ne.

Josephine Adeh ta ƙara da cewa tuni rundunar ta ƙara girke jami’an ‘yansandan da kayan aiki a faɗin birnin da kewaye.

A baya-bayan nan birnin na Abuja ya fuskanci karuwar matsalar garkuwa da mutane.

88 thoughts on “Babu wani shirin kawo hari jami’ar Abuja—Ƴansanda

  1. Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me?

Comments are closed.