October 18, 2025

An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da za a yanke hukuncin zaɓen gwamnan Bauchi da Kano

FB_IMG_1700208992400.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

An tsaurarantsaro a harabar kotun ɗaukaka kara da ke babban birnin tarayya Abuja yayin da kotun ke shirin yanke hukunci a kan zaɓuɓɓukan Jihar Kano da Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa wasu hanyoyin da ke kan hanyar zuwa kotun an rufe su.

Ƴan jarida sun shaida cewa akwai ɗimbin magoya bayan da ke ƙoƙarin samun damar shiga harabar.

Jami’an ‘yan sanda da ke ƙoƙarin dakile karuwar magoya bayan sun yi amfani da barkwanon tsohuwa don tarwatsa su.

1 thought on “An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da za a yanke hukuncin zaɓen gwamnan Bauchi da Kano

Comments are closed.