January 15, 2025

Matashi a Bauchi ya kashe budurwarsa a kan naira 5000

3
image_editor_output_image-2076183278-1703134810093.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Bauchi a Arewacin Najeriya na nuna cewa wani matashi ɗan shekaru 19 mai suna Mohammed Ibrahim, mazaunin Sabon-Layi da ke wajen birnin Bauchi a Jihar Bauchi, ya daba wa budurwarsa mai suna Emmanuella Ande wuka har lahira.

Ahmed Mohammed Wakil, kakakin rundunar ƴan sanda Jihar Bauchi, shi ne ya sanar da faruwar lamarin cikin wata takarda manema labarai a garin Bauchi.

A cewar Wakil, hakan ya faru ne bayan wata sa-in-sa da aka samu a tsakaninsu kan kudi naira 5,000.

Rahotannin sun cewa kafin faruwar lamarin, Mohammed ya sace kusan naira 400,000 na mahaifinsa domin ya kashe wa Emannuella, wadda ‘yar Jihar Filato ce, bayan sun shirya haduwa a Fatakwal a Jihar Ribas.

Matashin da a a halin yanzu yana hannun ‘yansanda.

Ya kuma haɗu da marigayiyar ne a shafukan sada zumunta kafin daga bisani suka hadu a wani wurin shakatawa da ke unguwar Bayan-Gari a Bauchi.

Takardar Wakil ta ce, ““Wannan mummunan al’amari ya faru ne a lokacin da wadda aka kashe ta bukaci kudi naira 5000 yayin da ita budurwar ta nemi ya biya ta wasu da ta ke bin sa, hakan ne ya sa cacar-baki ta kaure har fads ya shiga tsakaninsu lamarin da ya yi sanadin da ya sa ta samu rauni wanda ya kai ga mutuwarta.

“Ya daba wa budurwarsa Emmanuella Ande ‘yar Jihar Filato, wuka a kusa da kirjinta, a lokacin ne budurwar ta yi kururuwa, mutanen da ke wajen suka yi yunkurin kai mata dauki, suka bude kofar da karfi, inda wanda ake zargin ya kuma daba wa daya daga cikinsu wuka.

“Tawagar ‘yansanda ta yi gaggawar kai dauki, inda suka dauki budurwar zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi, inda aka tabbatar da mutuwarta.”

3 thoughts on “Matashi a Bauchi ya kashe budurwarsa a kan naira 5000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *