October 18, 2025

AIKI GA MAI ƘARE KA: Dakarun Najeriya sun halaka wani ƙasurgumin ɗan ta’adda

images-2023-09-22T094527.720.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe wani ɗan bindiga da ya yi ƙaurin suna a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Ya ce an kashe ɗan fashin mai lakabin Mai-Nasara ne a wani samame da jami’an tsaro suka kai dajin Sangeko a jihar Kebbi.

An kuma kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan kungiyar ta Mai-Nasara ne yayin samamen.

Malam Idris ya ce, AbdulRahman Usman, daraktan tsaro a ofishin majalisar zartarwa na Birnin Kebbi ya bayyana nasarar da aka samu.

Yayin da yake yabawa da irin namijin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na yaki da miyagun laifuka a jihar, musamman a kudancin Kebbi, Malam Usman ya yi kira ga jama’a da su bai wa jami’an dukkanin goyon baya da hadin kai domin samun nasara.