Gwamnan Edo Ya Yi Alkawarin Biyan Diyya Ga Iyalan Mutum 16 Da Aka Kashe a Uromi

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi alkawarin ba da tallafi ga iyalan mafarauta 16 da wata kungiya ta tsaro ta kashe a Uromi, Jihar Edo.
Rahotanni sun bayyana cewa mamatan suna kan hanyarsu ta zuwa Kano ne lokacin da lamarin ya faru.
Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamatan a garin Torankawa, Jihar Kano, tare da takwaransa na Kano, Abba Kabir Yusuf.
“Muna shirin samar da diyya ga dukkan iyalan da abin ya shafa,” in ji Gwamna Okpebholo.
Ya jinjinawa al’ummar Kano saboda zaman lafiya da suka kiyaye duk da wannan mummunan lamari.
“Ina kuma yaba wa mutanen Jihar Kano da daukacin Arewa bisa hakuri da biyayya, wanda ya hana su daukar fansa kan wannan al’amari,” in ji shi.
Gwamnan ya yi addu’a ga mamatan tare da tabbatarwa iyalansu cewa za a yi adalci.