Gwamnatin Nijar Ta Ayyana Hutun Kwana 3 Don Makokin Mutum 44 Da Aka Hallaka
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar fararen hula 44 a wani hari na ta’addanci da aka kai kauyen Fambita da ke yankin Tillabéri.
Gwamnatin kasar ta danganta wannan farmaki da mayakan ƙungiyar ta’addanci ta Islamic State in the Greater Sahara (ISGS).
Masanin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.
A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gida ta Nijar, harin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da Musulmi ke tsaka da ibada a cikin watan Ramadan.
Maharan da suka zo dauke da manyan makamai sun kewaye masallacin kafin su kai farmaki.
An kuma tabbatar da cewa mutane 13 sun jikkata, ciki har da hudu da ke cikin mawuyacin hali.
A sakamakon wannan hari, gwamnati ta ayyana kwanaki uku na makoki daga ranar Asabar, 23 ga watan Maris, tare da umartar a sauke tutocin kasar rabi.
Ministan harkokin cikin gida na wucin gadi, Janar Salifou Modi, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa, “Wannan mugun aiki an aikata shi ne a ranar Juma’a, rana mai alfarma ga Musulmi, a cikin kwanaki goma na karshe na watan Ramadan.”
Ya kara da cewa wannan hari ya nuna cewa “’yan ta’adda da mabiyansu ba sa kiyaye kowanne irin darasin addini.”
Gwamnati ta sha alwashin cewa “wadannan manyan laifuka ba za su wuce ba tare da hukunci ba,” tana mai alkawarin gano wadanda suka kai harin, masu daukar nauyinsu da kuma masu ba su kariya domin a gurfanar da su a gaban kuliya.




