October 18, 2025

Abba da Gawuna: Malamai sun yi kira ga Kotun Ƙoli da ta yi adalci a shari’ar zaɓen gwamna

IMG-20231209-WA0078.jpg

Daga Ɗanlami Malanta

Wasu daga cikin shugabannin addinin Musulunci da suka nuna damuwarsu game da Jihar Kano sun gargadi Kotun Ƙoli da kar ta yi watsi da muradin al’umma a daidai lokacin da ta ke shirin yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar nan da ‘yan kwanaki.

Sai dai kungiyar malaman addinin Islama karkashin jagorancin Sheikh Nasiru Jibrin, ta nesanta kanta daga duk wani rikici da ka iya tasowa dangane da hukuncin da ke tafe.

Malaman Musulunci sun ba da shawarar cewa bai kamata a yi zalunci ba “a kan umarnin jama’a.”

Jagororin Musulunci nsun fito ne daga kungiyoyin Tijjaniyya, Kadiriyya, da Izala.

Sun kuma yi kira ga masu ruwa da tsakin da cewa, “ka da su karkatar da muradin al’ummar jihar Kano da suka fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’ar zaben gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) na jihar Kano.

“Tige Gwamna Abba na iya haifar da fushin da bai kamata ba a tsakanin daukacin al’ummar jihar, wadanda suka nuna soyayya ga Gwamnan. Kuma wannan fushin na iya haifar da rikici a jihar,” in ji kungiyar.

Kakakin kungiyar, Sheikh Jibrin, ya yi ikirarin matsayinsu ya yi daidai da na sauran malaman.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya jaddada cewa, “Ya kamata a bar Gwamna Abba Yusuf ya ci gaba da ayyukan alheri da ya fara tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, muna da ‘ya’yanmu duka a jihar, kuma ba za mu so duk abin da zai haifar da tashin hankali ba.”

Shi ma a nasa jawabin, Sheikh Sani Maharazu ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi adalci kuma ya yi aiki da gaskiya gabanin hukuncin Kotun Ƙolin a jihar.

Ya yaba da rawar da gwamna Yusuf ya taka wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar.

“Hakika gwamnan ya yi aiki tare da ‘yan sanda domin kare jihar, tare da tabbatar da tsaftace ta daga masu satar waya da sauran laifuka. Mun yaba da irin wannan karamcin da Gwamnan ya nuna na biyan wasu daliban Jami’ar Bayero Kano kudaden makaranta,” inji shi.