October 18, 2025

Sabon Tsari: Yanzu Dalibai Sai Sun Nuna Kundin Bincikensu Na Gama Jami’a Kafin Su Tafi Bautar Ƙasa

NYSC

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga yanzu duk ɗalibai da suka kammala karatun digiri a Najeriya ko ƙasashen waje dole ne su mika aikin binciken karatu (thesis ko project) zuwa ma’ajiyar NERD kafin su shiga shirin bautar ƙasa (NYSC).

Wannan sabon tsari na daga cikin sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su a ƙarƙashin dokar NYSC.

Manufar ita ce dakile amfani da takardun bogi da kuma tabbatar da ingancin shaidar karatu.

Sanarwar ta bayyana cewa daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, ba za a ɗauki wani ɗalibi ko a tura shi hidima ba sai dai idan ya gabatar da shaidar bin wannan umarni.

Sai dai tsarin ba zai shafi waɗanda suka riga suka shiga hidima ko waɗanda aka ɗauka kafin wannan rana ba.

A cewar gwamnatin tarayya, wannan mataki zai taimaka wajen kare ilimin ƙasa, dawo da martaba ga takardun karatu, tare da bai wa ɗalibai da malamai damar samun kuɗaɗen shiga daga binciken da aka mika.