October 18, 2025

Peter Obi Ya Ce Zai Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

images (83)

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, tare da alkawarin yin wa’adi daya kacal idan ya samu nasara.

Obi ya fitar da wannan jawabi ne ta bakin mai magana da yawun Peter Obi Media Reports, Ibrahim Umar, cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin a birnin Abuja.

Ya ce yana cikin tattaunawa da wasu jam’iyyu kan batun kafa kawance da nufin ceto Najeriya daga mawuyacin halin da kasar ke ciki.

A cewarsa, “Ban taba shiga wata tattaunawa kan hadin gwiwar tikitin takara da kowa ba, har da Atiku,” ya nanata.Obi ya bayyana cewa idan aka samu matsaya wacce za ta takaita mulkinsa zuwa shekara hudu kacal, zai amince da hakan, tare da ficewa daga kujerar shugabanci nan da ranar 28 ga Mayu, 2031.

“Ina goyon bayan duk wata kawance da za ta mayar da hankali kan dakile kashe-kashe a jihohin Benue da Zamfara, farfado da masana’antu, inganta tattalin arziki da ciyar da al’umma. Idan ba haka ba, kada a hada ni da irin wannan kawance,” inji shi.

Obi ya kara da cewa zai tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar nan kafin a cika shekaru biyu da fara shugabancinsa.

Dangane da rikicin cikin gida a Labour Party, ya bayyana cewa suna aiki kafada da kafada domin tabbatar da sahihancin shugabancin Nenadi Usman bisa hukuncin Kotun Koli, tare da neman amincewar hukumar INEC.