October 18, 2025

Ganduje Ya Ajiye Muƙaminsa A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa

images (78)

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka daga muƙaminsa bayan kusan shekara biyu yana jagorantar jam’iyyar a matakin ƙasa.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar wa manema labarai cewa Ganduje ya mika takardar murabus ne bayan da aka umarce shi da yin hakan daga fadar shugaban ƙasar.

“Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis), aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus. A yau da safe (Jumma’a) ya miƙa takardar,” in ji majiyar.

Saukar Ganduje na zuwa ne kasa da mako guda bayan rikicin da ya barke a taron jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas, inda wasu mambobin jam’iyyar suka nuna fushinsu kan kin bayyana mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai kasance tare da Tinubu a takarar shugaban ƙasa ta 2027.

A halin yanzu dai ba a fitar da sunan wanda zai maye gurbin Ganduje ba, sai dai ana sa ran jam’iyyar za ta gudanar da wani taron gaggawa don cike gurbin.