October 18, 2025

Ƴansanda sun kashe masu garkuwa da mutane da Suka Nemi Fansa na Naira Miliyan 40

FB_IMG_1729278603506.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

‘Yan sanda a jihar Enugu sun kashe wasu mutum biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane yayin wani samame da suka kai a maboyarsu dake Nokpa-Nike, sannan suka ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi.

Wanda aka yi garkuwa da shi, wani mai taimaka wa sanannen mutum a jihar, an sace shi ne a ranar 27 ga watan Satumba, inda aka nemi fansa ta naira miliyan 40.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya ce jami’an sun kwato bindiga G-3 daya, bindigogi AK-47 guda biyu, tare da mujallu da alburusai 125.

Ana zargin wadannan mutanen da hannu a hare-haren yin garkuwa da mutane da dama, sannan har yanzu ana ci gaba da neman sauran masu garkuwar da suka tsere.

Kwamishinan ‘yan sanda, Kanayo Uzuegbu, ya yaba wa jami’an ‘yan sanda bisa wannan nasara, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da tsaro a ko da yaushe.

17 thoughts on “Ƴansanda sun kashe masu garkuwa da mutane da Suka Nemi Fansa na Naira Miliyan 40

Comments are closed.