Masarautar Bauchi ta hana wasannin kilisa na doki a unguwannin garin
Daga Sabiu Abdullahi
Masarautar Bauchi ta sanar da dakatar da duk wasu nau’ikan wasan dawaki da matasa ke yi (Kilisa) a dukkan anguwannin da ke cikin garin Bauchi, daga jiya Juma’a, 18 ga Oktoba, 2024.
Wannan matakin ya biyo bayan korafe-korafen kuntata wa al’umma da kuma hatsarorin da ke faruwa yayin gudanar da irin wadannan wasanni.
Sanarwar ta fito ne a karkashin sa hannun Magatakardan Majalisar Sarkin Bauchi, Alhaji Shehu Mudi Muhammad.
Masarautar ta gargadi duk wanda ke da bukatar gudanar da irin wannan aiki da ya nemi izini daga majalisar Sarki.
Duk wanda kuwa ya saba da wannan umarni za a dauki matakin doka a kansa.