October 18, 2025

Ƴansanda sun kama saurayin da ya yi ƙaryar an yi garkuwa da shi

IMG-20240407-WA0004.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta, a ranar Alhamis, ta gurfanar da wasu mutane 12 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da wani yaro dan shekara 17 da ya yi ƙaryar an sace shi a yankin Agbor da ke jihar.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Asaba, babban birnin jihar, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abaniwonda Olufemi, ya bayyana cewa matashin ya riga ya ɓarnatar da kudin da aka ba shi a matsayin fansa kafin a kama shi.

Am ambato shi yana cewa, “A ranar 20 ga Maris, 2024, rundunar DPO Agbor ta samu korafi a kan zargin sace wani yaro dan shekara 17 (wanda aka sakaya sunansa) a Okumera quarter, Agbor-Obi.

“Wanda ake zargin ya aika wa ‘yar’uwar sa sakon murya inda ya bayyana cewa an yi garkuwa da shi, kuma masu garkuwar suna neman naira miliyan 1.”

“Bincike ya nuna cewa matashin mai shekaru 17 ya hada baki da abokansa tare da yin karya wajen sace shi.“

2 thoughts on “Ƴansanda sun kama saurayin da ya yi ƙaryar an yi garkuwa da shi

Comments are closed.