Lalle Natenyahu yana tafka kura-kurai a hare-haren da yake kaiwa Gaza—Biden
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Benjamin Netanyahu, wanda shi ne firaministan Isra’ila yana matuƙar tafka kurakurai a hare-haren da Isra’ilar ke kaiwa a zirin Gaza.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da sashen Sipaniyanci da ke kasar Amurka da ake kira Univision
A cewar BBC, Biden ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza da suka yi sanadiyyar mutuwar ‘yan agaji guda bakwai abun ‘tayar da ghankali ne, inda ya yi kira da a tsagaita wuta.
Hirar ta mista Biden wadda ke da tsawon awa guda an nade ta ne ranar Larabar da ta gabata kuma aka watsa ta ranar Talata da daddare.
Shugaban Amurka dai ya shahara wajen mara wa Isra’ilar baya a yakin da take yi da Falsɗinawa.